Labarai Siyasa

Ƙarya kawai Atiku yake shirgawa ‘yan Najeriya akan bashin da muke ci -Minista

Tun da fari, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana Najeriya na biyan bashin kaso 99 cikin dari na kudin shiga, inda yayi nuni da cewa a farkon shekarar nan Najeriya ta samu biliyan N950.56 inda kuma ta biya bashin biliyan N943.12.

Rahoton DABO FM ya bayyana Ministan yada labarai, Lai Mohamed ya yi martani kan kalaman Atiku da sanyin safiyar Laraba, na cewa tsohon mataimakin shugaban kasar karya kawai yake fadawa yan Najeriya.

Lai yace “Kalaman da Atiku keyi ba komai bane illa fatan Najeriya ta fada matsanancin hali, kuma har yanzu mun rasa gano inda ya samo alkaluman mun biya bashin biliyan N943.12 kana kuma mun sami kudin shiga biliyan N950.56 a farkon shekarar nan ba.”

Ya kara da cewa “Daya daga cikin abinda yasa kudin shiga keyin kasa shine dogaro da man fetir kawai da kasar keyi.”

Zuwa yanzu dai bashin da ake bin Najeriya ya kai Biliyan Dubu N27.4 kamar yadda aka bayyana a Disambar 2019.

Karin Labarai

Masu Alaka

‘Yan Najeriya su cire Rai da samun tsaro a gwamnatin Buhari – Mungadi

Dabo Online

2023: Akwai yiwuwar rugujewar APC bayan mulkin Buhari -Fayemi

Muhammad Isma’il Makama

Buhari ya dora alhakin hare-haren kisan kiyashi na ‘yan ta’adda a Arewa kan annobar Korona

Muhammad Isma’il Makama

An fara zanga-zangar kifar da gwamnatin Buhari, Jami’an tsaro su kawo dauki -Uzodinma

Muhammad Isma’il Makama

Kotu ta watsar da bukatar Atiku na bincikar kundin tattara sakamakon zaben 2019 daga INEC

Dabo Online

Na’urar tattara zabe ta INEC ta nuna Atiku ne ya lashe zaben 2019 – PDP

Dabo Online
UA-131299779-2