Aisha Buhari ta halarci taro da rigar naira miliyan 1.6

Uwar gidan shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta saka abaya mai tsadar dalar Amurka 4,290, kwatankwacin Naira Miliyan 1,565,850.

DABO FM ta binciko cewa, kamfanin dake dinkin rigunan yana da zama a kasar Indiya.

Rigar mai suna MAPLE LEAF EMBROIDERED SILK-CREPE CAPE-BACK CAFTAN, ana siyar da ita a shagunan yanar gizo-gizo, kamar su Oscardelarenta da sauran manya manyan shagunan dillancin kayayyakin sakawa masu tsada.

Garzaya wannan shafin domin siyan taku rigar, ko kuma ganewa idanuwanku ko tanadi ga masu aure na kusa.

Danna akan jan layin

DANNA ANAN
DANNA ANAN DON GARZAYAWA SHAFIN SIYAR DA RIGUNAN

Aisha Buhari, ta kasance mai ta’ammali da kayyakin sakawa masu tsada, wanda bincike ya nuna a shekarun baya, ire-iren kayyaki masu tsada da take sanyawa yakan janyo ce-ce kuce a kafofin sadarwar musamman a Instagram.

Masu Alaƙa  Iyalan Buhari na da damar daukar jirgin shugaban kasa suyi harkokin gaban su -Garba Shehu
Lokacin da Aisha Buhari take sanye da kayan.

Daga shagunan siyar da rigunan.

Daga Shagon Siyar da rigar.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.