An kashe sifeton yan sanda yayin ba-ta-kashi da yan bindiga a Imo

Karatun minti 1

Yan bindiga sun kai hari a wani babban ofishin ofishin yan sanda da ke Mgbidi a jihar Imo.

Rahotanni sun ce an kashe Sifeton yan sanda tare da ji wa yan sanda da dama raunuka.

Yan bindigar sun afka wa ofishin yan sandan ne a daren ranar Juma’a, lamarin da ya tada hankalin al’ummar yankin sakamakon ba-ta-kashin da aka yi da jami’an ‘yan sandan.

Wata majiya ta shaida wa Jaridar Punch cewa yan bindigar sun je ofishin yan sandan ne a kan babura. Majiyar ta ce yan bindigar su na zuwa su ka fara barin wuta.

Sai dai majiyar ta ce yan sandan da ke bakin aiki sun tsayar da yan bindigar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dan sandan da kuma raunata wasu daga ciki.

Da ya ke tabbatar da faruwar al’amarin, kakakin rundunar yan sandan jihar, Micheal Abattam ya ce jami’an hukumar da ke bakin aiki sun tare harin yan bindigar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog