An sace ɗalibin Jami’ar BUK a Kano

Karatun minti 1

Kungiyar daliban jami’ar BUK ta tabbatar da batan ɗaliban jami’ar mai suna Shafi Auwal Muhammad.

DABO FM ta tattara cewar ɗalibin ya na shekararshi ta biyu ne a  jami’ar in da ya ke karantar Fasahar Ilimin Fetur.

Sanarwar ƙungiyar daliban mai dauke da sa hannun shugabanta na riƙon ƙwarya, Sen Auwal Lawan Nadabo ta ce ƙungiyar ta bayar da cigiyar neman dalibin tin bayan da ta samun labarin ɓatan ɗalibin.

Ta ce sun tuntuɓi abokanshi na makarantar da kuma abokan karatunshi, duk sun tabbatar da ba su ganshi a makarantar ba tin kafin ranar Alhamis.

Da su ke sanar da sashin Hausa na Jaridar Daily Nigerian, iyayen ɗalibin sun ce rabonsu da ɗan nasu tin ranar Alhamis bayan ya fito domin tafiya makaranta.

Iyayen sun ce su na zaton an sace ɗalibin ne a tsakankanin titin Tsohuwar BUK zuwa Sabuwar BUK.

Sun kuma bayyana cewar har kawo yanzu ba a tuntubesu game da dan basu ba, ba su kuma samu labarinshi ba kuma duk lambobinshi na waya ba sa tafiya.

Iyayen na sa sun ce har yanzu ba a tuntuɓe su ta waya a kan Muhammad, ko gano inda ya ke ba.

Ƙungiyar daliban jami’ar  ta ce duk wanda ya gan shi ko ya samu wani labari a kan sa to ya tuntuɓi 08064178848.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog