Ana cigaba da jimamin rasuwar Dr Ahmad BUK

dakikun karantawa

Al’ummar Musulmin Najeriya da ma dukkanin Muslimin duniya masu jin yaren Hausa, su na cigaba da jimamin rasuwar babban malami Dr Ahmad Ibrahim Muhammad Bamba.

An bayyana mutuwar babban malamin a matsayin wani rashin wanda ba za a taba maye gurbinshi ba.

Malamin dai ya rasu a jiya Juma’a, 7 ga watan Janairun 2022 a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke jihar ta Kano bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Malamai da dama sun nuna alhinunsu a yayin da su ka gabatar da hudubar Juma’a, yayinda al’umma su ka karaɗe kafofin sada zumunta da yi masa addu’a.

DABO FM ta tattara cewar; mutuwar Sheikh Ahmad BUK, mutuwace da a wannan zamanin ba ayi mutuwar da ta karade shafukan sada zumunta kamar ta shi ba.

A shashin Story na Whatsapp, daga jiya, babu abin da mutum ya ke gani sai hotuna da gutsuren karatuttukan malamin. Kusan mutum ya kan samu cewa dukkanin abokan huldarshi sun yi wa malamin addu’a.

Sheikh Muhammad Bn Uthman, babban limamin masallacin Sahaba da ke jiyar Kano, ya bayyana malamin a matsayin babban rashi na al’ummar Musulmin duniya, ya kuma ce da wuya a sake samun wanda zai maye gurbinshi.

“Wannan ta’aziyya ce gaba daya ga duniya Musulunci. Mutuwa irin ta gama-gari ba ta buya balallantana ta gagara-gari. Hadisan Annabi Muhammad SAW, shekaru 30 cur.

In kana da iliminshi, to ai ba ka da lokacinshi, in kana jin kana da lokacinshi, ba ka da shekarunshi, in kana da shekarunshi, ai ba ka da gogewa da gwagwarmayarshi. Haka Allah ya ke kayanShi, baiwarShi, to ga shi kuma an dauke.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog