Labarai

Baɗala da ɗalibai: An saki farfesa bayan zaman shekaru 2 kacal a gidan yari

An saki wani babban farfesan sarrafa lissafin kudi daya amsa laifin neman yin lalata da wata dalibarsa ta jami’ar Obafemi Awolowo University (OAU) dake garin Ile-Ife, Richard .

Rahoton DABO FM dai ya tabbatar da tin wancan lokacin da ya amsa laifinsa kuma babbar kotun tarayya dake garin Osogbo, jihar Osun karkashin hukuncin alkali, Maureen Onyetenu ya daure shi bayan amsa laifukan da aka zarge shi tin cikin shekarar 2018.

Kotun dai ta daure shi wata 12 bisa neman bata dalibar sa, sa’annan wani karin wata 12 saboda goge maganganun da suka yi a kafar sadarwa ta WhatsApp. Inda da farko shekara 6 akayi tinanin za’a daure shi.

Karin Labarai

UA-131299779-2