Bata gari sun kone ofishin PDP a Kano

Bayan gudanar da babban gangami na tarbar dan takarar shugabancin kasa inuwar jami’iyyar PDP jiya Lahadi a birnin Kano.

Rahotanni sun nuna wasu bata gari da ake zargin ‘yayan jami’iyyar APC ne sun kone ofishin jami’iyyar PDP dake unguwar Ciranci a karamar hukumar Gwale ta birnin Kano.

Saidai har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar basu bada tabbacin faruwar al’amarin ba.

Manema labarai sun nemi jin ta bakin babban mai hulda da jama’a na rundumar amma abin yaci tira.

%d bloggers like this: