Labarai

Bincike ya nuna Ƴan Majalisar Tarayya na Kano ɗumama kujera suke a Habuja

Bincike ya tabbatar da kafatanin yan majalisar tarayya na jihar Kano zaman dumama kujera suke a majalisar kasar dake babban birnin tarayya Abuja.

Binciken na Dabo FM dai ya gano yan majalisa biyu ne rak daga nan Kano suka shiga jerin sunayen yan majalisar da suka fi kai kudiri a shekarar da ta shude 2019, inda sauran da baa bayyana sunayen su ba suka gaza shiga jerin masu kwazon majalisar.

A tsawon watanni shida kacal da kafuwar wannan majalisa mai tsawon zangon shekaru hudu nan gaba, ‘yan majalisa 269 cikin ‘yan majalisar wakilai 360 sun gaza gabatar da kudiri ko da guda daya ne. Kamar yadda LeadershipAYau ta bayyana.

A zuwa watan disambar shekarar 2019,  ‘yan majalisu 91 suka gabatar da kudurori 499. Tun bayan kafa majalisa ta tara (9th Assembly) a ranar 11/6/2019,  daga cikin daukacin kudurori 688 da aka gabatar,  ‘yan majalisar wakilai sun gabatar da kudurori 499, a yayin da takwarorinsu na majalisar dattawa suke da kudurori 189.

A tsawon watanni shida kacal, Dan Majalisar Wakilai na Tarayya, mai wakiltar Karamar Hukumar Zariya, a inuwar jam’iyyar APC, Dafta Abbas Tajuddeen, ya kafa tarihin zama wanda ya fi yawan  gabatar da kudiri a Majalisar dokoki ta Tara.

An bayyana Dan majalisar, Honarabul Abbas Tajudeen, a matsayin wanda ya fi yawan kudiri da guda 33. Wadanda ke biye da shi a baya sun hada da; Mai tsawatarwa a majlisa, Honarabul Mohammed Tahir Monguno (APC, Borno) da Honarabul Dachung Musa Bagos (PDP, Plateau), wanda suke bi masa da kudiri 27 kowanne su.

Wanda daga cikin su tuni wasu kudurorin an riga an samu su hannu sun zama doka, a yayin da wasu daga cikin kudurorin tuni sun riga sun tsallake siradin karatu na daya, na biyu da kuma na uku. A binciken da aka gabatar, daga cikin kudurori 91 da aka gabatar a majalisa, ya nuna cewa jam’iyyar APC mai rike da ikon majalisa, na kan gaba da kudurori 48, a yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ke biye mata da kudurori 36.

A yayin da jam’iyyun APGA, ADC, APM, ke da kudurori guda daya daya kacal.  Sauran jam’iyyun da har a zuwa wannan lokaci sun gaza gabatar da kudiri guda daya kacal, sun hada da jam’iyyar AA, LP, PRP, da kuma jam’iyyar SDP.

Kakakin majalisa, Femi Gbajabimila (APC, Lagos) wanda ke da kudiri goma 19,  Honarabul Gideon Luca Gwani (PDP, Kaduna) mai kudiri goma 15, sai kuma mataimakin Kakakin majalisa, Honarabul Ahmed Idris Wase (APC, Plateau) wanda ke da kudiri 10,

Honarabul Dan Agundi Munir (APC, Kano), Honarabul Abdulrazak Namdas (APC, Adamawa) suke da kudiri 7. Masu biye dasu da kudirori hudu sun hada da; Honarabul  Yusuf Buba Yakub (APC, Adamawa), Honarabul  Jonathan Gaza (PDP, Nasarawa), Honarabul  Ali Abdullahi Ibrahim (APC, Kogi), Honarabul  Abubakar Suleiman Gumi (PDP, Zamfara), Honarabul Abdullahi Saidu Musa (APC, Niger).

Masu kudurori 3 sune; Honarabul Mohammed Umar Jega (APC, Kebbi), Honarabul Aishatu Jubril Dukku (APC, Gombe), Honarabul Ali Mohammed Wudil (APC, Kano), Honarabul Alphonsus Longgap (APC, Plateau) da kuma Honarabul John Dyegh (APC, Benue).

Sauran dake da kudurori 2 su ne;  Honarabul Zainab Gimba (APC, Borno), Honarabul Olawuyi Abdulraheem Olatunji (APC, Kwara).

Mai rike da mukamin Shugaban masu rinjaye , Honarabul Peter Akpatason (APC, Edo) shi ke jagorantar sauran masu kudurori 1 kacal, tare da Honarabul Thomas Ereyitomi (PDP, Delta).

Karin Labarai

Masu Alaka

Yayin dokar hana fita, an kama jami’in Karota a tube tare da wata yarinya Kano

Dabo Online

Taskar Matasa: Ga wanda suke tunani mai kyau, Daga Umar Aliyu Fagge

Katsina: Gidauniyar Kwankwasiyya zata kafa asusun fitar da dalibai karatu kasashen Duniya

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu-Yanzu: Mahaifin matashin da baturiya ta biyo Kano zai kai maganar gaban jami’an tsaro na ‘SSS’

Muhammad Isma’il Makama

Da alama jami’an kula da ‘Gidan Zoo’ a Kano sun tsare kudin da aka tara da Babbar Sallah daga Goggon Biri

Dabo Online

Wallahi munyi aringizon ƙiri’u a Kano, – Wani Jagoran APC a Kano

Dabo Online
UA-131299779-2