A daren jiya Lahadi wayewar yau Litinin wasu mahara dauke da muggan makamai suka kai hari jami’ar Maiduguri. Maharan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne, sun shiga makarantar wajen karfe 10:00 na dare. Maharan sun shiga da ababen hawa kimanin Guda 10. Sun yi ta harbe-harbe cikin iska,Continue Reading

Kotun daukaka kara ta mayar wa da Ibrahim Baba na APC kujerar sa a Filato. Duk da matsalar tsaro, za a gudanar da zabukan kananan hukumomi a ranar 27 ga watan Afrilu a jahar Zamfara. Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali ya ce furucinsa baya nufin kaskanta sarakunan gargajiya. ‘Yan bindiga sunContinue Reading

Gidauniyar Ilimi ta Kwankwasiyya na neman dalibai dasuka kammala Digiri na farko domin turasu yin digiri na biyu  a kasashen waje. A cigaba da shirin da gidauniyar takeyi na bunkusa Ilimi, gidauniyar ta shirya wajen daukar nauyin karatun Dalibai domin karo karatu a kasar waje. Daliban da suka gama DigiriContinue Reading

Gwamnatin Tarayya ta rabawa masu sana’ar aski guda 20 ‘yan asalin yankin Niger Delta Naira miliyan 88 a matsayin tallafi karkashin hukumar dake yiwa ‘yan yankin afuwa. Ko wanne daga cikin wadanda suka amfana da shirin, zai samu Naira miliyan 4.4 a matsayin tallafin. A takarda mai lamba PRO/SAP&CAP/TOVO/2019/0010/V/C.1009, wacceContinue Reading

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Abdulaziz, tace zata dauki matsafa 1,700 domin samarwa jihar zaman lafiya. Gwamnatin ta bayyana haka ne ta hannun Kwamishinan kananan hukumomi na jihar, Alhaji Bello Dankande, a wani taro da yayi da Sarakunan gargajiyar jihar. “Kowacce masarauta zata samu mutum 100 hadi da 500Continue Reading

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta yi nazari dangane da harajin barasa da Kamfanukan dake sarrafa ke yi, kuma za ta duba yiwuwar rage harajin. Wannan matakin rage harajin akan barasar ya zo ne bayan watanni 17 da gwamnatin shugaba Buhari ta karawa barasar da tabar sigari haraji da kashiContinue Reading