Da Ɗumi Ɗumi: Jami’an EFCC sun daƙume dan takarar PDP yana tsaka da siyan ƙuri’a

Karatun minti 1

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC sun damke dan takarar jamiyyar PDP lokacin da yake tsaka da siyan kuri’a a bakin akwatun zabe na karamar hukumar Isiala Mbano dake jihar Imo.

Majiyar Dabo FM ta tabbatar da afkuwar hakan, inda da isarsu akwatun zaben Umucaram Amaraku suka tarar da dan takarar PDP, Obinna Onwubuariri ya baje hajarsa.

TheCable tace ta jiyo daya daga cikin jamian na bayyana cewa an aike musu da sakon karta kwana ne na dan takarar yana wannan mugun aiki.

Tini suka yi awon gaba dashi zuwa ofishin su inda sukayi kokarin tafiya da dan sandan da yake kula da lafiyar sa sai dai jamian soji sun shiga tsakani, Obinna dai shine dan majalisar tarayya mai wakiltar Okigwe North.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog