Dubban matuka Adaidata Sahu sun je gaishe da mahaifiyar Barr Abba Hikima

Karatun minti 1

Dubban matuka Adaidata Sahu sun je gaishe da mahaifiyar Abba Hikima

Matukan baburan Adaidata Sahu na jihar Kano sun yi cikar kwari zuwa gaishe da mahaifiyar Barr. Abba Hikima Fagge, DABO FM ta tabbatar.

Barr Abba Hikima Fagge, shi ne lauyan da ya shiga tsakanin domin sasanci tsakanin Hukumar Karota da matuka baburan a tataburzar da ta wakana tsakaninsu.

Da ranar yau Asabar, matukan a adadi da ido ba ya misaltawa sun shiga unguwar Fagge, mazabar Fagge D1 domin su gaishe da mahaifiyar Barr. Abba Hikima a matsayin ziyarar nuna godiya.

Yayan Barr Hikima, Sheikh Ibrahim Hikima ya bayyana farin cikinshi game da ziyarar da matuka babura su ka kawo wa mahaifiyar tashi.

Ya ce; “Yau munyi baki da yawan gaske a gidanmu. Kungiyar yan adaidaita sahu na Kano sun zo gaishe da mahaifiyarmu dalilin Bar. Abba Hikima.”

“Allah ya kiyayeku ya baku mafita ya warware wa al’ummar Musulmi matsalolinmu albarkar MA’AIKIN ALLAH (sallallahu taala alaihi wa ala alihi wasallam).”

Kalli bidiyon a kasa:

Karin Labarai

Sabbi daga Blog