/

Ganduje na cikin jerin gwamnonin dake fuskantar barazanar tsigewa daga kotun ƙare kukan ka

dakikun karantawa

Jerin gwamnonin dake fuskantar barazanar tumbuke wa daga babbar kotun kasa wadda ke karkashi babban mai sharia na kasa, CJN Tanko Muhammad.

Rahoton da Dabo FM ta hada ya bayyana cewa kimanin gwamnoni 5 ke jiran hukuncin babbar kotun, inda gwamnonin da magoya bayan su suke cikin dari-dari.

Yanke hukunci akan shari’ar zaben gwamnan Sokoto da jami’iyyar APC ta take kalubalanta ya samu tasgado bayan da hayaniyar mutane tayi saka alkalan ficewa daga dakin gabatar da shari’a, inda bayan kusan sa’a guda, magatakarda a Kotu ya sanar da dage yanke hukunci zuwa ranar Litinin.

A zaman da Kotun kolin tayi a jiya Talata, karkashin jagorancin Alkalin Alkalan Najeriya, Tanko Muhammad, ta ayyana dan takarar gwamna na jami’iyyar APC, Hope Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar inda ta tsige gwamna dake kan mulki, Mista Emeka Ihedioha.

Shari’ar jihar Kano da jihar Sokoto, itace shari’ar da take daukar hankulan al’umma musamman saboda rudanin dake cikinta.

A tsagin masu goyon bayan gwamnatin jihar Kano hadi da lauyoyinsu, na ganin nasara na bangarensu bisa dalilinsu na samu nasara da sukayi a kotunan baya tare da cewar suna ganin an gudanar da zaben ranar 9 ga watan Maris bisa doran doka bayan soke akwatina sama da 200 da baturen zaben Kano, Farfesa Riskuwa yayi.

Inda a banagaren PDP da dan takarar ta, Abba Kabiru Yusuf, take iya da “ayi mata adalci” domin a cewar ta, an soke akwatina da aka sake zabe a kansu ba bisa ka’ida ba, tare da cewar baturen zaben jihar bashi da ikon soke akwati a wajen tattara sakamakon zabe.

Sai dai alamu sun nuna kowanne bangaren siyasar jihar Kano, yana cike da kwarin gwiwar samun nasara. A wani bangaren, magoya bayan PDP sun bayyana cewar “Karfin gwiwarsu” yafi na tsagin gwamnatin biyo bayan hukunci da kotun ta yanke a kan zaben Imo inda aka mayarwa da dan takarar APC wasu kuri’unshi da aka soke.

Sai dai DABO FM ta tattara cewar bayan soke kuri’un Kano, an sake gudanar da zabe inda a jihar Imo, ba’a sake zabe ba.

Sauran gwamnonin sun hada da gwamnan Bauchi, Bala Muhammad Kauran Bauchi, gwamnan Binuwai, Samuel Utom da gwamnan Filato, Simon Lalung.

Tini dai an sanya ranat Litinin 20 ga Junairu domin yanke hukuncin zaben Kano tsakanin dantakarar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusif da Abdullahi Umar Ganduje wanda ya tsaya karkashin jam’iyyar APC.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog