Ginin babban dakin karatun Abuja zai lakume Naira biliyan 50 – Ministan Ilimi

Ministan Ilimin Najeriya, Malam Adamu Adamu, yace za’a kashe kimanin naira biliyan 50 wajen karasa ginin babban dakin karatu dake garin Abuja.

Ministan yace gwamnatin shugaba Buhari zata bazatayi kasa a gwiwa ba wajen karasa duk wani aikin da ta gada daga gwamnatocin da suka shude.

A shekara 2006 aka fara kaddamar da shirin ginin akan kudi naira biliyan 8, a shekarar 2013 aka kara cire naira biliyan 18 wajen farfado da aikin. a cewar malam Adamu Adamu.

An kiyasta kashe naira biliyan 78 kafin daga bisani kudin ya zama biliyan 50 bayan sake duban kudin.

%d bloggers like this: