Copyrighted.com Registered & Protected

Gwamnan babban Bankin Najeriya ‘CBN’ da wasu ma’aikata sun sace Naira Biliyan 500

A cikin wannan faifan sauti muryar Gwamnan Babban bankin Najeriya, CBN Godwin Emefiele da mataimakinsa, Edward Lametek Adamu da kuma daraktan kudi, Dayo M. Arowosegbe da daya daga cikin mai bayar da shawara na musamman a CBN suna tattaunawa kan yadda za’a yi rufa-rufa a wata badakalar Naira bilyan 500 da aka sace a CBN don gudanar da wani kasuwanci na kashin kai da ya nemi ya tashi.

Daga tashar Sahara Reporters. Bidiyo kashi na 1

Za’a iya ganin tallar da Dabo FM ba tada hurumi akai.

Faifan sautin dai guda biyu da SaharaReporters suka samu suka kuma sanya, yana dauke da yadda gwamnan na CBN da manyan jami’an bankin suka yi wadakata da wadannan kudaden wanda aka yi asararsu a harkar kasuwanci da aka yi asararsa a Dubai.

A cikin sautin an ji Emefiele yana fadawa mataimakinsa, Adamu da ya ya yi kokarin kaucewa duk wata matsala da ka iya faruwa, da gwamnati za ta yarda ta bayar da tsabar kudi na Naira bilyan 100 amma kuma gwamnatin ta ki yarda. A saboda haka za su iya bankado su.

A cikin faifan gwamnan CBN yana nuna tsoronsa da fargaba idan ‘yan adawa suka gano wannan badalakar, sai mataimakinsa yake nuna masa cewa babu matsala kawai za a san yadda za a yi rufa-rufa ta yin la’akari da matsalar tattalin arziki da kasa ke fama da ita. 

Kashi ba 2.
Za’a iya ganin tallar da Dabo FM ba tada hurumi akai.
%d bloggers like this: