Copyrighted.com Registered & Protected

Gwamnan CBN ya ware biliyan 2 domin toshiya ga EFCC bayan ya sace biliyan 500

Jaridar Sahara Reporters ta rawaito cewa; gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya ware naira biliyan 2 domin dankawa hukumar yaki da masu ta’annatin tattalin arzikin kasa ‘EFCC’ a matsayin toshiyar baki.

Hakan na zuwa ne bayan ‘yan kwanaki da jaridar ta cire wasu faifayen murya wanda aka ji gwamnan bankin yana tattaunawa da mataimakinshi akan yacce sukayi amfani da kudaden.

Sai dai jaridar tace har yanzu hukumar ta EFCC bata ce komai a game da faifayen muryar ba.

Babban bankin CBN din ya tabbatar da sahihancin wayar, sai dai bankin yace gwamnan yana magana ne akan wata biliyan 150 na basussukan da suke bawa wadansu yan kasuwa.
 
Jaridar ta tabbatar da zancen da hukumar CBN din tayi bashida tushe, domin a cikin faifan muryar an jiyo gwamnan bankin yana cewa ‘yana kokari ne don ganin sun dawo da kudin kafin a gane.

%d bloggers like this: