//
Wednesday, April 1

Hukumar Hisbah ta chafke wani babban Ɗan Sanda a ɗakin otal tare da mata 3

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar Hisbah ta chafke wannan dan sanda ne da kannensa 2 da kuma wata da yace daga Kaduna take cikin dakin otal suna sheke ayarsu.

Kakakin Hukumar, Dr Atiku Zawuyya ne ya bayyana hakan lokacin da yake baje kolin wanda ake zargin a garin Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Dr Atiku ya sanar da Dabo FM cewa “Da muka tsaurara bincike mun gano mata 2 daga ciki yan uwane na jini ga shi dan sandan, wanda yake aiki a babbar caji ofis ta garin Gusau.”

Ya kara da cewa “1 yarinyar kuma yar garin kaduna ce, mun jima muna jan kunnen masu wannan otel amma sunyi kunnen kashi.”

Masu Alaƙa  Wasu daga Sarakunan gargajiya na da hannu a rikicin arewacin Najeriya - Minista

Daga karshe dai hukumar ta hada da manajan otel din, inda hukumar tace zata mika su kotu idan ta kammala binciken ta. Kamar yadda DailyTrust ta fitar.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020