Jami’an Gwamnatin Kano sun ki halartar Jana’izar Bashir Tofa

Karatun minti 1

A safiyar yau Litinin aka yi jana’izar Alhaji Bashir Tofa, daya daga cikin dattawan jihar Kano kuma tsohon dan takarar shugabancin Najeriya a zaben 1993 a gidanshi da ke unguwar Gandun Albasa da ke birnin Kano.

DABO FM ta tattara cewa rahotanni da kuma shaidun gani da ido sun tabbatar da rashin ganin keyar wakili daga fadar gwamnatin jihar Kano.

Marigayi Alhaji Bashir Tofa ya kasance mai yawan kalubalantar gwamnatin Dr Abdullahi Ganduje kan wasu kudure-kudurenta da ya ke wa kallon ba za su amfani al’umma ba.

Daga cikin wadanda su ka halarci jana’izar akwai Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Sanata Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano, Alhaji Sabo Nanono, tsohon Ministan Noma da sauran manyan mutane.

Sai dai gwamnatin ta fitar da sanarwar ta’aziyyarta a shafukan sada zumunta.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog