Makarantar Sheikh Umar Sani Fagge ta horar da ma’aurata 202 karo na 10

Karatun minti 1

Makarantar horar da ma’aurata ta Sheikh Prof. Umar Sani Fagge ta yaye dalibai 202 a karo na 10.

Makarantar da ta ke horar da ma’aurata maza karkashin cibiyar yaɗa addinin Musulunci ta Abu Ayubal Ansari mallakin Prof Umar Sani Fagge ta sake yaye dalibai ma’aurata da masu yin aure kwana kusa a karo na 10.

DABO FM ta tattara cewar an yaye daliban su 202 bayan samun horo na kusan makonni 12 a jiya Alhamis a unguwar Fagge.

Ana gudanar da karatun ne a Dandalin Fagge da ke kwaryar Fagge a karamar hukumar Fagge.

Taron ya samun halartar Farfesa Umar Sani Fagge, Sheikh Ibrahim Khalil, Farfesa Kamilu Sani Fagge, Alhaji Isa Haruna, shugaban ‘yan Koli na kasuwar Sabon Gari, tsohon kakakin majalisar Kano, Rt Hon Abdullahi Yusuf Ata da sauran manyan baki.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog