Man City ta ragargaje Chelsea (6:0)
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester city ta ragargaza takwarta ta Chelsea da ci shida da nema a yammacin yau Lahadi.
Wasan da aka buga a birnin Manchester, ya baiwa kungiyar ta Manchester City damar darewa kan teburin gasar Premier League ta kasar Ingila.
Dan wasa Raheem Sterling, shine ya fara jefawa Manchester City kwallo a minti na 4, yayinda Sergio Aguero ya jefa ta biyu a minti na 13.
Raheem Sterling (minti na 4, 80)
Sergio Aguero (Minti na 13 , 19, 16(P))
Ilkay Gundogan (Minti na 25)
Wannan ne karo na farko da mai horarwa na kungiyar ta Chelsea, Sarri yasha babban kayin da aka zura masa kwallo shida a raga.
Yanzu dai Chelsea ta koma mataki na shida, Manchester United kuma tana mataki na hudu.