/

Masu zanga-zanga sun tare wa Firaminista Indiya, Narendra Modi hanya

Karatun minti 1

Masu zanga-zanga a garin Hussainiwala da ke birnin Ferozepur a jihar Punjab ta Indiya sun tare wa Firaminista hanyar saukowa daga gadar sama.

Rahotanni sun ce Firaminista Modi ya shafe kusan minti 20 a kan gadar saboda masu zanga-zangar sun tare hanyar saukar.

DABO FM ta tattara cewar tsaikon da aka samu ya tilasta wa Modi soke zuwa wajen taron yakin neman zaben yan jami’iyyarsu da zai je.

Sai dai tsagin jami’iyyar BJP, jami’iyyar Firaministan sun yi Allah-wadai da abin da su ka kira jin kunya ga gwamnatin jihar Punjab kan rashin tabbatar da tsaro duk da sanin zuwan Firaministan.

Ana ganin masu zanga-zangar manoma ne da su ka shafe sama da shekara su na nuna borensu ga wata sabuwar doka da gwamnatin Modin ta sanyawa harkar noma a kasar.

Kazalika wasu ‘yan jami’iyyar BJP sun zargi gwamnatin jihar da jami’iyyar Congress ta ke mulka da kitsa makarkashiya domin hana Modi zuwa wajen taron.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog