Matasa sun kone motocin APC a Abuja

Majiya tace adadin motocin da aka kona sukai kimanin guda 9, a wata babbar hanyar zuwa unguwar Dei-Dei dake babban birnin tarayyar Abuja.

Lamarin ya faru ne bayan wani dan hargitsi daya barke tsakanin matasan jami’iyyar PDP da APC a yau Lahadi.

Wani matashi, mai rahoton gani da ido yace, masu yawan kamfen din APC suna tafiya ne zuwa gaisuwa wajen Sarkin unguwar Dei-Dei a lokacin da yan jami’iyyar adawar ta PDP suka far musu.

Tini dai ‘yan sanda suka bayyana a wannan waje domin kwantar da tarzoma tare da kama wadanda suke da hannu acikin rikicin.

Shugaban jami’iyyar APC na gari Abuja yace, lallai akwai babbar barazana ta rashin tsaro idan a haka za’a gudanar da zabe.

Ana yawan samun rikice-rikice a tsakanin matasa mabam-banta ra’ayoyin siyasa a Najeriya, musamman a wannan lokaci da babban zaben kasar bai wuce kasa da kwanaki bakwai ba.

%d bloggers like this: