Labarai Siyasa

Matawalle ya bi gidajen talakawa marasa karfi da tallafin ₦500,000 kowannen su

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle Muradun ya bi gida gida da tallafin naira dubu dari biyar ga kowanne talaka da Allah ya tsaga da rabonsa a cikin garin Gusau dake jihar ta Zamfara.

Rahoton da ya iske mu a nan Dabo FM ya tabbatar mana da cewa yanzu haka gwamnan yana bi gida gida da wannan tallafi na makudan kudi wanda a jihar ba’a taba yinsa ba.

Ziyarar da suka kira da ta bazata wato ‘Operation taimakon Talaka har cikin turaka’.

Yanzu dai mutane da yawan gaske sun anfana da wannan tallafi wanda banda Allah san barka babu abinda suke, ga baki har kunne da farin ciki gami da abin tausayi.

Tin dai bayan hawan mulkin jihar da gwamnan yayi, al’umma jihar suke ta samun alfanu daga gwamnatin wacce ta kudiri aniyar tabbatar da zaman lafiya a jihar baki daya.

A kwankin baya, lokacin gwamnatin da ta shude, jihar Zamfara ta kasance wata matattara ta barayin shanu da masu garkuwa da mutane wanda yayi sanadin mutuwa da gudun hijirar dubban mutane.

Karin Labarai

Masu Alaka

Abdulaziz Yari ya mikawa Matawalle takardun mulkin jihar Zamfara

Dabo Online

Duk shifcin-gizo gwamnoni keyi a batun biyan Sabon Albashi -Kungiyar Kwadago

Muhammad Isma’il Makama

Bayan biliyan 1 na gyaran makabartu, Matawalle zai gina sabon gidan gwamnati na biliyan 7

Dabo Online

“Kuna kan gwaji na wata 3” -Gov Matawalle ga sabbin Kwamishinoni da Masu Bada Shawara

Muhammad Isma’il Makama

Ta’addanci: Duk randa Abdulaziz Yari ya sake zuwa Zamfara, da kai na zan kama shi – Matawalle

Dabo Online

A kalla ‘Yan Gudun Hijira 25,000 suka koma Gidajensu na ainahi a jihar Zamfara

Dabo Online
UA-131299779-2