Labarai

Mawaƙan ‘Buhari Jirgin Yawo’ sun ga ta kansu a hannun wani ɗan siyasa

Da misalin karfe 2:00 na dare ranar Lahadi, wasu da ake zargin yan daban siyasa ne , sun je garin Gwadangaji dake jihar Kebbi suka dauko Mawaki Bello Bala Aljannare daga gidansa.

Rahoton mu na nan Dabo FM bayyana cewa sunyi awon gaba da shi mawakin zuwa gidan wani dan siyasa a cikin Birnin Kebbi.

Inda ya fuskanci dukan fitar albarka har da barazanar kisa kamar yadda ya shaida mana.

Hakazalika an balle dakin Otal da sauran mawakan suka sauka a cikin garin Birnin Kebbi kuma aka dauko su aka kaisu gidan wannan dan siyasa da karfe 3 na dare.

Aka kai Bello Aljannare, tare da wasu mawakan, su ma a nan ne suka sha dan banzan duka na fitan hankali.

Majiyarmu ta samo cewa an yi masu wannan duka ne sakamakon wata wakar diban albarka da Mawakan suka yi ma wani babban dan siyasa da kuma shugaba Buhari a jihar Kebbi.

Lamari da ya tayar da kura ganin yadda dubun dubatan mutane suka mallaki wannan wakar cikin yan kwanaki kalilan.

Karin Labarai

Masu Alaka

Zaben Gwamnoni: Ku zabi gwamnonin da jam’iyyar APC ta tsayar takara kawai – Buhari

Dangalan Muhammad Aliyu

Shugaba Buhari zai bar Najeriya zuwa kasar Chadi a safiyar yau

Dabo Online

Yanzu Yanzu: DSS ta cafke mutumin da ya fito da labarin auren Buhari

Muhammad Isma’il Makama

APC ce ta lashe zaben Kano kuma ta tabbatarwa Kotu – Buhari

Dabo Online

Dama can nasan Ganduje ne yaci zaben Kano -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Buhari zai jagoranci raba motocin zirga-zirga 820 a jihar Legas

Dabo Online
UA-131299779-2