Mun bar barayi da Allah – Buhari

Shugaba Muhammad Buhari yace hukuncin duk masu sace kudin al’ummar yana wajen Allah.

Shugaban yayi bayanin ne jiya juma’a, a dakin taro dake fadar gwamnatin tarayya dake abuja, taron da yayi da wata kungiyar magoya bayanshi ta ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje.

Yace gwamnatin PDP tayi mulki har na tsawon shekaru 16, lokacin da ake siyar da gangar danyen mai sama da miliyan biyu a rana, kan kudi sama da $120 kowace ganga, amma babu abinda zasu iya nunawa a matsayin wani gagarumin aiki da sukayiwa al’ummar Najeriya.

Shugaban ya kara da cewa, a shekarar 2015 da suka karbi mulki, Najeriya babu tituna, hanyoyin jirgin da wutar lantarkni da aka cire kimanin dala biliyan 16 ($16 billion) domin tabbatar dasu.

“Naje babban banki kasa (Central Bank of Nigeria), akacemin babu kudi”

“Wadanda zamu iya daukar mataki akansu, zamu hukuntasu, sauran kuma sakamakonsu yana wajen Allah. Duk abinda muka samu damar dawo dashi, zamu siyar mu saka kudin a cikin baitul mani don amfanin kasa.

Shugaban yace ya tsaya a matsayinshi domin yin aiki tukuru wajen kare Najeriya da dukiyar ta.

%d bloggers like this: