Mutane sun fara suma, kafin zuwan Kwankwaso da Atiku filin Sani Abacha

:for English and other languages , please use the translator at the footer of this page.

Yau ne ake gangamin taron jami’iyyar PDP a jihar Kano a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata.

Wakilinmu da yake filin taron a yanzu ya shaida cewa mutane sun fara suma saboda rasa wajen tsayiwa tin kafin isowar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Alhaji Atiku Abubakar.

Mutanen waje suna kokarin shiga filin taron, ciki ya cika , na waje suna son shigowa.

Karfe 3:58 a lokacin da muke tattara bayanai, har ila wannan lokaci basu samu halartowa ba.

Bayanai suna shigowa yanzu…

%d bloggers like this: