Sakamakon zaben Gama ya ɓace ne a cibiyar tattara sakamako dake karamar hukuma – Baturen Zabe

Baturen zaben mazabar gama dake karamar hukumar Nassarawa ta jihar, Joshua Kubai, ya bayyana a gaban kotun korafe-korafen zaben gwamnan jihar Kano domin amsa tambayoyi a cigaba da gudanar da shari’ar da PDP ke kalubalantar zaben Dr Ganduje.

Kotun ta gayyaci Kubai, ma’aikaci a jami’ar Bayero dake Kano biyo bayan bukatuwar lauyoyin jami’iyyar PDP da dan takararta Abba Kabir Yusuf.

Kubai wanda ya bada shaida bayan duban tsanaki da lauyoyin wadanda ake kara sukayi tare da bincikar takardar rantsuwar bada shaida da Kubai yayi.

Ya bayyana cewar takardun sakamakon zaben mazabar Gama “Sun bace” a cibiyar tattara sakamakon zabe dake karamar hukumar Nassarawa.

Da yake yi wa manema labarai bayani, daga cikin lauyoyin PDP, Maliki Kuliya, ya bayyana jin dadinsu bisa yacce Baturen zaben da yayiwa INEC aiki ya zo ya bada shaida akan abinda kalubalanta – a cewarshi.

A nashi bangaren, lauyan Dr Abdullahi Ganduje , ya ce suna da kwarin gwiwa ganin yacce lamarin yake tafiya.

%d bloggers like this: