Labarai

Wasu ‘Ɓata-Gari’ sun afkawa jama’a tare da farfasa motoci fiye da 20 cikin dare a Kano

An wayi gari da ganin wani abin takaici da fargaba a unguwar Marmara dake cikin gari a jihar Kano, bayan da wasu da ake zargin ɓata-garin matasa ne suka afkawa al’ummar unguwar da sara tare da farfasa motoci da keke nafe dake kwana a gefen kwalta, fiye da motoci 20 ake fargabar abin ya shafa.

Majiyar Dabo FM tayi ido biyu da motoci ciki harda baburin ‘Adaidaita Sahu’, abin ya faru ne a daren Talata, inda mutanen unguwar ke cikin fargaba tare da rashin sanin takamaiman abinda ya haddasa wannan barna.

Har zuwa yanzu dai babu rahoton chafke wadanda suka tafka wannan barna.

Karin Labarai

UA-131299779-2