‘Yan daba sun kai hari, gidan shugaban APC na jihar Kano

Hukumar ‘yan sandan jihar Kano ta bada tabbacin harin da wasu matasa suka kai gidan shugaban jami’iyyar APC ja jihar Kano, Abdullahi Abbas.

DSP Haruna Abdullahi Kiyawa, mai magana da yawun rundunar yace, matasa da ake zargi ‘yayan jami’iyyar PDP ne, sun kai harin ne a hanyarsu a zuwa yawon kamfen.

“Sun raunata mutane da dama tare da faffasa gilasan motoci kusa da wajen.”

Haruna Kiyawa, yace an tura jami’iyya domin kwantar da tarzoma tare da tabbatar da zaman lafiya saboda faruwar hakan anan gaba.

%d bloggers like this: