Manyan Labarai Najeriya

Zuwan Buhari Kano: Barranta rashawa ko goyon bayanta?

Jirgin yakin neman zaben shugaba Buhari yau zai sauka a jihar Kano, jihar da ake zargin gwamna Abdullahi Ganduje da karbar rashawa.

Gwamnatin shugaba Buhari, gwamnati ce da ke yakin da masu cin hanci da rashawa, sai dai wasu musamman yan jami’iyyar adawa suna fadin cewa gwamnatin na yakar wadanda basa goyon bayan gwamnatin.

Shin shugaba Buhari zai nuna goyon bayanshi ga gwamna Abdullahi Ganduje? Itace tambayar da al’ummar kasar suke jira daga shugaban.

Barrantar shugaban kasar daga goyon bayan gwamnan, zatayi nuni da tabbas gwamnatin tashi na yakar duk wasu masu cin hanci da rashawa koda kuwa suna tare a inuwar jami’iyya daya, ‘yan adawa kamar jami’iyyar PDP kuma ka iya cewa duk jirgi daya ne ya dauki gwamnatin jihar Kano dama gwamnatin shugaba Buhari, idan har ya goyi bayan gwamna Ganduje.

A kwanaki baya tsohon shugaban kasar, Chief Olusegun Obasanjo yace

“Dan jam’iyyar APC zai iya sace dukiyar Najeriya gaba daya, kuma babu abinda zai faru dashi, dan jami’iyyar PDP kuwa idan ya saci Naira Goma ko bayan shekara goma ne sai ya dawo da ita”.

Masana shiyasa suna ganin yau alhamis 31/01/2019 itace fadan karshe na tabbatar da gaskiyar shugaba Muhammad Buhari.

Masu Alaka

‘Yan Najeriya sun yanke hukunci, NNPC ta huta?, Buhari yaci zabe.

Dangalan Muhammad Aliyu

Daga kin gaskiya: Matashin daya sha ruwan kwata akan Buhari bai mutu ba.

Ko Sheikh Zakzaky zai warke a kasa da kwanaki 1416 da suka ragewa Buhari da El-Rufai?

Dabo Online

Kwabid19: Zamu gwada daukacin Almajiran Kano – Ganduje

Dabo Online

Bama samun Wutar Lantarki sai kazo Daura – Masarautar Daura ta fadawa Buhari

Dabo Online

Ganduje yayi alkawari mayar da karatun Firamare kyauta da daukar nauyin karatun masu bukata ta musamman

Dabo Online
UA-131299779-2