4
Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da kama wani magidanci mai suna Peter Sinamai mai shekaru 40 bisa zargin hallaka mahaifinshi tare da jefa shi cikin rijiya.
Rundunanar ta hannun mai magana da yawunta ta ce ta samu nasarar fito da gawar mahaifin da ɗan ya jefa a rijiyar ƙauyen da ke kusa da su na Sangere da ke Ƙaramar hukumar Gombi a jihar Adamawa.
Ya ce binciken da rundunar da gudanar ya nuna cewar sai da Peter ya hallaka mahaifin nashi kafin daga bisani ya jefa shi cikin rijiyar a ƙoƙarinshi ya ɓoye laifin da ya aikata.
DABO FM ta tattara cewar tuni dai aka fito da gawar mutumin kuma a ka aiketa zuwa ɗakin ajiyar gawa domin gudanar da binciken musababbin mutuwar mutumin, kamar yadda Sahara Reporters ta bayyana.
