Fitaccen mawakin Afrika, David Adeleke, ya bayyana cewa idan a ka yi magudi a zaben gwamnan jihar Osun na wannan shekarar, zai kai ƙara wajen shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump
Davido ya bayyana haka ne a wani shirin kai tsaye da ya yi da dan wasan barkwanci, Cater Efe.
A ranar 15 ga Agusta 2026 ne dai za a gudanar da babban zaɓen gwamna a jihar Osun.
Kanin mahaifin mawakin, wato Gwamna Ademola Adeleke, ya na neman tazarce a kujerar gwamnan jihar da ya ke kai yanzu a jami’iyyar Accord.
Gwamnatin jihar ta na zargin gwamnatin shugaba Tinubu da yi mata maƙarƙashiya, zargin ya ƙara karfi bayan da EFCC ta rufe asusun gwamnatin jihar gabanin zaɓen.
Sai dai tuni shugaba Tinubu ya umarci EFCC ta nemi kotu ta amince domin a buɗe asusun gwamnatin jihar da a ka rufe.
