Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, ta rufe asusun bankin gwamnatin jihar Osun na bankin First Bank, kwanaki 10 kafin babban zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 15 ga Agusta 2026.
Jaridar Vanguard ta rawaici cewar ta ga wasu takardu da ke tabbatar da an sanya wa asusun gwamnatin jihar takunkumin ‘Post No Debit.’
Post No Debit: Na nufin cewar kuɗi za su iya shiga cikin asusun amma mai asusun ba zai iya amfani da kuɗin da ya ke ciki ba, ta kowacce hanya. Ba za a iya cirar kudin ta ATM ba, ba za a iya tura wa wani kuɗi ba. Kai tsaye dai, duk kuɗin da aka sanya a cikin asusun, ba za a iya cirewa ba.
Sai dai tin a kwanakin baya, gwamnan jihar, Ademola Adeleke ya zargi EFCC da yunƙurin rufe wa gwamnatin jihar da wasu manyan jami’an gwamnatin asusun bankunansu.
Wani makusancin gwamnatin da ya nemi a sakaye sunanshi, ya tabbatar da rufe asusun, ya ce kuma nan ba da jimawa ba gwamnan zai yi manema labarai cikakken bayani a kan lamarin.
