Akalla mutane 18 sun nutse yayin tsere wa harin yan ta’adda a Sokoto

An samu nasarar ceton mutane 7 da ransu, sai dai har yanzu ba a ga mutane 18 ba, lamarin da ya sanya a ke fargabar cewar sun rasu.

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Ana fargabar cewa akalla mutum 18 sun rasa rayukansu bayan wani kwale-kwale ya kife da su yayin da suke ƙoƙarin tserewa harin ‘yan ta’adda a ƙauyen Tsamaye, da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addar sun kai harin ne a daren Litinin, inda suka shafe sa’o’i da dama suna cin karensu babu babbaka a ƙauyen. Haka kuma, an ce sun yi garkuwa da mutane 37.

Mazauna yankin sun bayyana cewa da zarar suka ji ‘yan ta’addar sun kutsa cikin garin, mutane da dama suka ruga zuwa bakin ruwa domin tsallakawa su tsira da rayukansu.

A cikin firgici da rudani, mutane da yawa sun hau kwale-kwalen fiye da ƙarfin da zai iya ɗauka. Mafi yawan waɗanda suka shiga kwale-kwalen mata ne da ƙananan yara. Rahotanni sun ce kwale-kwalen ya kife ne yayin da yake ɗauke da mutane kusan 25.

Wani mazaunin garin ya ce:

“Da muka kira ‘yan uwanmu ta waya, ‘yan bindigar ne suka ɗauki wayar suka ce sun yi garkuwa da mutane 37.”

Rahotanni sun kuma bayyana cewa mata da ƙananan yara na cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00