Tallar Tinubu ta sa an dakatar da wasan cikar Abba Gida-gida shekaru 3 a kan mulki

An dakatar da wasan ƙarshe na gasar cikar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, shekara uku a kan mulki bayan wasu magoya bayan APC sun shiga filin wasa ɗauke da hotunan Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Abba, lamarin da ya haddasa kwaranyowar yan kallo zuwa cikin filin.

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

An dakatar da wasan ƙarshe na gasar “AKY @ 3 Years”, wato gasar cikar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, shekara uku a kan mulki, wadda Ali Na Yara ya shirya ƙarƙashin kulawar Gidauniyar Kwamishinan Muhalli da Ruwa na jihar Kano, Dr Dahir Hashim.

Ana buga wasan ne tsakanin ƙungiyoyin Fagge Professional da Brigade Professional, wanda shi ne wasan ƙarshe a gasar da aka shafe makonni ana bugawa tsakanin manyan unguwannin jihar Kano. An buga wasan ne a filin Shinge da ke unguwar Kurna a cikin birnin Kano.

Sai dai, shigowar wani jagoran APC da magoya bayan jam’iyyar APC ya tilasta dakatar da wasan, wanda a ka shafe makonni ana jiran ranar bugashi a yau Alhamis, 6 ga Agusta 2026.

An buga wasan sama da minti 20, amma babu ƙungiyar da ta zura ƙwallo, inda aka ci gaba da wasa da sakamakon 0-0.

A yayin wasan, an bai wa ɗan wasan Fagge Professional, Halifa Carvalho, katin gargadi.

Wasan, wanda DABO FM ta halarta, ya zo ƙarshe ne lokacin da wasu tarin magoya bayan da a ke zaton wakilin Kwamishinan Muhalli da Ruwan Sha na Jihar Kano, Dr. Dahir, suka shigo filin yayin da a ke tsaka da gudanar da wasan.

Da suka shiga filin tare da magoya bayansu, suna ɗauke da hotunan Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf, sun kutsa har cikin filin wasan tare da ganguna ana kaɗa kiɗa.

Lamarin ya sa wasu daga cikin ’yan kallo su ma suka shiga cikin filin domin nuna rashin goyon bayansu ga shigowar ɗan siyasar.

Hakan ya sa ‘yan wasan suka nemi a dakatar da wasan, kasancewar filin ya cika da jama’a.

A filin wasan akwai tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, da ɗan wasan tsakiyar Kano Pillars, Rabiu Ali, tare da sauran fitattun ’yan wasan Kano da ke taka leda a ƙasashen Turai.

Domin ganin yadda ta kasance a bidiyo:

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00