Shugaban kasar Ghana- Akupo-Addo
Labarai

Kwabid-19: Shugaban kasar Ghana zai gina asibitoci 88 cikin kwana 365

Domin shawon kan karancin asibitoci a kasar Ghana, shugaban Nana Akufo-Addo, ya sha alwashin gina sabbin asibitoci na zamani har guda 88 na zamani cikin kwanaki 365.

Hakan na zuwa ne bayan matsalar da yace kasar ta gani bisa rashin wadatattun asibitoci a yanayin da ake ciki na barkewar annobar Kwabid-19.

Shugaban ya bayyana haka ne a jawabin da ya yiwa al’ummar kasar karo na 8 kan halin da ake cikin dangane da kokarin gwamnati na yakar annobar coronavirus, da kuma matakan da take dauka wajen aiwatar da dabarun dakile cutar, kamar yadda sashin Hausa na gidan Radio Faransa ya rawaito.

Tin dai a ranar 15 ga watan Maris, kasar ta Ghana ta sanya dokar hana tarurrukan jama’a dai dai lokacin da aka tabbatar da wasu mutane 2 sun kamu da cutar Kwabid-19.

Zuwa yanzu shugaban ya tsawaita dokar ta hana fita a ranar Litinin zuwa wasu makonni biyu masu zuwa.

Karin Labarai

UA-131299779-2