Fursuna mai jiran hukunci kisa ya yi ‘Live’ a Tiktok, an sauke jami’ai 3 a kan lamarin

by Dabo Online
0 comments

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) ta sauke jami’in da ke kula da Gidan Yarin Ibara da ke Abeokuta, Jihar Ogun, tare da wasu manyan jami’ai biyu, bayan wani fursuna da ke zaman jiran aiwatar da hukuncin kisa ya yi amfani da wayar hannu wajen shiga TikTok Live.

Dabo FM ta bayyana cewar, Fursunan, Elijah Oyebode, an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a shekarar 2019, bayan Babbar Kotun Jihar Osun ta same shi da laifin kashe Rofiat Adebisi, wata ɗalibar shekarar ƙarshe a Jami’ar Jihar Osun.

Rahotanni sun ce Oyebode ya kasance yana da asusun TikTok mai yawan mabiya, inda wani daga cikin asusunsa ya kai matakin Level 20 na karɓar kyaututtukan kuɗi yayin bidiyon kai tsaye.

Hukumar NCoS ta ce binciken farko ya tabbatar da cewa fursunan ya mallaki wata wayar hannu da aka haramta amfani da ita a gidan gyaran hali, kuma ya yi amfani da ita wajen shiga kafafen sada zumunta.

Hukumar ta ce an kwato wayar yayin wani samame, kuma yanzu tana hannun jami’an bincike a matsayin hujja.

Bugu da ƙari, an mayar da Oyebode zuwa wani gidan gyaran hali inda aka sanya shi ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro, yayin da ake ci gaba da bincike.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Hukumar NCoS, Chief Superintendent of Corrections JN Osuji, ya fitar ranar Alhamis, hukumar ta bayyana lamarin a matsayin babban gibi na tsaro da kuma keta ƙa’idojin aikin gidajen gyaran hali.

Hukumar ta ce an cire jami’in da ke kula da Gidan Gyaran Hali na Ibara da wasu manyan jami’ai biyu daga muƙamansu, har sai an kammala binciken da ake gudanarwa.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00