Wata uwa ta siyar da jaririyarta a kan N2.9m, an ba ta N300,000 ba a cika mata ragowar ba a Anambra

by Dabo Online
0 comments

Hukumar SASA mai yaƙi da ayyukan da suka shafi tilastawa mutane aikata laifuka ta Jihar Anambra, tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Mata da Jin Daɗin Al’umma ta jihar, sun kama wata uwa da wata mata bisa zargin sayar da jaririyarta kan Naira miliyan 2.9 a garin Awada da ke ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra.

Mahaifiyar jaririyar, mai suna Miss Chioma, a yayin da ta ke ba da labarin abin da ya faru a lokacin da ta ke amsa tambayoyi a ofishin hukumar SASA A a ranar Juma’a, ta ce jim kaɗan bayan ta haihu, wata da a ke cewa Precious Uchenna, ta karɓi jaririyar, inda ta taimaka wajen shirya sayar da ita, tare da haɗin gwiwar wani mutum guda.

Ta ce Precious Uchenna wata malamar coci cea garin, kamar yadda Jaridar Punch ta rawaito.

Mahaifiyar jaririyar ta kuma bayyana cewa ta karɓi Naira 300,000 daga cikin kudin da aka siyar da jaririyar, yayin da Precious Uchenna, ta riƙe sauran kuɗin. Sai dai ta ce bayan an kammala cinikin, an kama mata gida kuma a gabanta a ka miƙa jaririyar ga wata mata wadda ba ta san sunanta ba.

Ita kuwa Miss Precious Uchenna, a nata ɓangaren, wanda a ke cewa ita ce babbar wadda ake zargi, ta ce; ta taimaka an siyar da jaririyar ne domin ta taimaka wa mahaifiyarta saboda ta na cikin mawuyacin hali da matsin rayuwa.

Da a ke tambayarta a kan dalilin da ya sanya ta ba wa mahaifiyar jaririyar N300,000 kacal daga kudin cinikin, ta yi shiru, ta kasa bayar da dalililin yin hakan, sai dai ta ce ka kama mata gida a lokacin da yan uwan matar su ka ki amincewa da cikin da ya ke jikinta.

Da yake magana da manema labarai bayan kammala tambayoyin, Manajan Daraktan Hukumar SASA ta Jihar Anambra, Monday Nwokoye, ya ce jami’an SASA sun kama waɗanda ake zargin ne tare da haɗin gwiwar al’umma, bayan tattara bayanan sirri sakamakon rahotannin da suka samu.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00