Wani magidanci ya koka kan yadda ya ce matarshi ta hana mahaifinta yi masa alheran da ya saba tin farkon aurensu, ya ce yana kiran al’umma da su saka baki matarshi ta taimaka ta bari mahaifinta ya cigaba da yi masa abubuwan alherin da ya saba.
Ya ce suna zaman lafiya tsakaninshi da matar shi har na tsawon shekaru 2, mahaifinta ya saba kusan duk shekarama a kasar Saudiyya su ke azumin Ramadana. Ya na daukarsu tare da sauran yan uwan matar su ma da mazajensu su zaga duniya, zuwa kasashe irinsu Hadaddiayar daular larbawa da kasar Amurka, kamar yadda ya bayyana da kan shi a shafin Northern Marriages a shafin Instagram.
Miji da ya roki a sakaya sunanshi, ya ƙara da cewa; bai san dalili ba ya ga an dai na yin tafiyar da shi.
“Har tafiyar da a ke yi duka dangin, ni yanzu an daina yi da ni. Wani lokacin ma sai ya rage saura kwana 1 tafiyar tasu ma ta ke sanar da ni a matsayina na mijinta. Kuma su sauran yan uwanta duk ana yin tafiyar tare da su da mazajensu.”
Ina aikin da na ke samun N230,000 a wata, amma sauran mazajen yan uwanta, su na aiki a NNPC, NPA da kuma masu kasuwancin miliyoyin nairori.”
Sai dai ya ce batun aiki, dama ita matar tashi ne ta yi masa alƙawari cewa mahaifinta zai sama masa babban aiki, idan ya yi mata magana yanzu, sai ta bar zancen.
“Lokacin da na samo ƙwarin gwiwata, na kira mahaifinta, sai ya ce min ai ta ce masa ni ba na buƙata, abin da na ke yi a yanzu ya ishe ni.”
Sai dai kwana 2 bayan saƙon da ya turo, ita ma matar a na ta ɓangaren ta yi martani kan iƙirarin mijin tare da bayyana dalilin da ya sa yanzu ba ta saka shi a harkokin gidansu.
“A shekarar aurenmu ta farko, ni ce na ke yin komai da kuɗina. Babu wani abu da ya ke saukewa na hakkokinshi na gida. Ni ce ko iyayena su ke biya mana duk ƙasar da mu ka taɓa zuwa.”
“Mahaifina ya canza wa ƴayanshi mota duk shekara biyu, haka ya saka mijina a cikin lissafin canjin motar.”
“Na buɗe masa shaguna, na zuba masa kaya, na bashi jarin sama da naira miliyan 20 amma ya na cinyewa. Babu abin da ya ke yi a shagon sai tara yan mata ya na musu ƙaryar shi mai kudi ne.”
Yanzu haka ma ni ina gida, kuma tin da ya zaɓi kawo maganar kafafen sada zumunta, ranar Litinin zai kai shi kotu a raba auren.”
