Mallam Ali Nuhu, fitaccen mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a kafafen sadarwa ya bayar da labarin yadda ta faru da shi tsakaninshi da wani jami’in hukumar FRSC a kan hanyarshi birnin Onitsha.
Ya bayyana cewar jami’in ya tareshi ne da zargin rashin ɗaura bel din kujerar mota.
DABO FM ta rawaito Mallam Ali Nuhu ya na cewa; “Na roki jami’in ya bar ni in tafi, na tabbatar masa cewar ba zan sake ƙin ɗaura bel din mota ba.”
Sai dai jami’in ya yi masa barazanar kwace lasisin tuƙinshi tare da aika motar zuwa ofishin hukumar.
Ya ce bayan ya yi ta roƙo, jami’in daga ƙarshe ya yanke shawarar karɓar N30,000 daga gare shi, wanda ya ce shi ne kaɗai kuɗin da yake da su, kuma kuɗin ne da zai yi amfani da su wajen sayen man fetur da sauran abubuwan da ya ke buƙata.
“Na ba shi kuɗin ina mai cike da baƙin ciki, amma haka dai na cigaba da tafiyata.”
“Ina dab da shiga Onitsha, sai na ji ƙarar waya kusa da ni, na yi mamakin ganin wata waya ƙirar Samsung Galaxy S24 a kan kujerar gefena.”
A cewarsa, ya ɗaga wayar ne kawai domin amsa kiran, inda ya gano cewa wayar ta jami’in FRSC ce da ya kasance a cikin motarsa, wanda ya manta da ita a ciki.
“Yanzu jami’in yana roƙonsa da ya mayar masa da wayar.
Ya ce: “Da kai ne a matsayina, me za ka yi?”
