‘Yan sanda sun gano kungiyar satar yara da safararsu, sun ceto yara 17 a jihar Oyo

by Dabo Online
0 comments

Rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo ta ce ta gano wata kungiyar masu sata da safarar yara tsakanin jihohi, inda ta ceto yara 17 tare da kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a lamarin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abimbola Olugbenga, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Eleyele, Ibadan.

Ya ce binciken ya fara ne bayan rundunar ta samu wata takarda koke, amma daga baya binciken ya bankado wata babbar matattara da ake zargi da satar yara, safarar su, sayar da su da kuma boye su.

Rundunar ta ce ɗaya daga cikin abubuwan da binciken ya gano shi ne zargin amfani da wasu sassan jikin yaran da suka mutu wajen yin tsafi.

Kwamishinan ya ce binciken ya kai ga kama wata mata mai suna Adejoke Popoola, wadda ake zargi da hannu wajen ɓacewar wani yaro mai shekaru uku, Ifakunle Ifagbenro, a wani bikin masquerade a garin Oyo.

A cewar rundunar, bayan kama Popoola, ta bayyana cewa tana da hannu wajen satar yara sama da 15, masu shekaru tsakanin biyu zuwa bakwai, daga wuraren ibada, bukukuwa da sauran wurare a Oyo da wasu jihohi.

‘Yan sandan sun kuma kama wata da ake zargi da kasancewa abokiyar aikinta, Adekanbi Janet, wadda aka gano a Mowe, Jihar Ogun. A can ne aka ceto yara hudu masu shekaru tsakanin biyu zuwa hudu da kuma wasu mata biyu masu juna biyu.

Daga bisani, binciken ya kai ‘yan sanda zuwa Agbor a Jihar Delta, inda suka ceto wasu yara hudu da ake zargin an sace su daga Oyo.

Rundunar ta ce kawo yanzu ta ceto yara 17, yayin da wasu yara shida suka mutu a hannun mutanen da ake zargi da satar su, kamar yadda Jaridar Punch ta bayyana.

‘Yan sandan sun kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi da amfani da gawar yaran da suka mutu wajen ayyukan tsafi.

Rundunar ta bukaci iyaye ko masu kula da yaran da suka bata a baya-bayan nan da su garzaya hedikwatar ‘yan sandan Oyo da ke Eleyele domin duba yaran da aka ceto da kuma taimakawa wajen mayar da su ga iyalansu.

‘Yan sandan sun kuma shawarci jama’a da su rika kai rahoton bacewar yara cikin gaggawa, tare da yin taka-tsantsan wajen barin wasu mutane su raba yara da iyalansu ko kai su wuraren da ba a bayyana ba.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00