Kano Pillars za ta fafata da ƙungiyar ƙwallon kafa ta Niger Tornadoes a wasa na mako na 2 a gasar Firimiya ta Najeriya.
Magoya bayan ƙungiyar za su iya samu damar shiga kallon ƙungiyar bayan takunkumin da aka sanya na hana kungiyar buga wasannin gida da yan kallo ya kare.
Magoya bayan kungiyar za su iya siyan tikitin zuwa kallon wasan ƙungiyar da za ta fafata ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano ta hanyar shiga shafin yanar gizo-gizon ƙungiyar.
Latsa nan (Koriyar kala): Shiga Shafin
