1
Mata uku sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Dam ɗin Tiga
KANO — Mata uku sun rasa rayukansu bayan kifewar wani kwale-kwale a Dam ɗin Tiga da ke ƙaramar hukumar Tudunwada a jihar Kano.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Asabar, lokacin da kwale-kwalen da ke ɗauke da matan ya kife, kamar yadda jaridar SolaceBase ta ruwaito.
Matan da suka rasu sun haɗa da Murjanatu, Atikatu da Bilkisu, waɗanda dukkaninsu ’yan asalin garin Yalwan Rugu-Rugu ne.
Shugabar ƙaramar hukumar Tudunwada, Hajiya Sa’adatu Salisu Soja, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana hakan a cikin saƙon ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta.
An ci gaba da tattara ƙarin bayanai kan musabbabin hatsarin da kuma ko akwai wasu mutanen da abin ya shafa.
