Home LabaraiKano: An samu ambaliyar ruwa a karamar hukumar Fagge

Kano: An samu ambaliyar ruwa a karamar hukumar Fagge

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

DABO FM ta tabbatar da cewa ruwan sama mai ƙarfi da aka yi ya haddasa ambaliya a wasu sassan ƙaramar hukumar Fagge da ke Kano, inda mazauna da dama suka fara ficewa daga gidajensu domin tsira.

Har zuwa lokacin da muke wallafa wannan labari, ruwan na ci gaba da shiga gidaje da shaguna a wasu unguwanni, lamarin da ya jefa mazauna cikin fargaba.

Mafi yawan wuraren da ambaliyar ta fi kamari sun haɗa da:
Layin Bashir Tashi
Layin Sama’ila Mai Guza
Kamfala
Layin Kwalta

Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa ruwa ya mamaye ƙasan layukan, gidaje da shaguna, lamarin da ya sa mutane da dama suka fara kwashe kayansu zuwa saman layukan domin tsira da rai da dukiyoyinsu.

DABO FM na ci gaba da bibiyar lamarin tare da tattara ƙarin bayanai. A bana, hukumomi sun riga sun yi gargaɗin cewa Kano na cikin jerin jiohin Kano da ke fuskantar barazanar ambaliya yayin damina.

A makon da mu ke ciki ma gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar NIHSA ta bayar da bayanan cewar akwai yiyuwar fuskantar ambaliya mai tsanani a wasu jihohi 17 a faɗin Najeriya.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00