Home LabaraiTattaunawa da yan ta’adda karfi za ta kara musu – Martanin Ganduje ga Kwankwaso

Tattaunawa da yan ta’adda karfi za ta kara musu – Martanin Ganduje ga Kwankwaso

by Dabo Online
0 comments

Tsohon shugaban jami’iyyar APC na Najeriya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce mayar da martani zuwa ga ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jami’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan wasu kalamansa na cewar idan sun samu gwamnati, za su yi ƙokari tattaunawa da kowa har da ‘yan ta’adda domin shawo kan matsalar tsaro.

Ganduje ya ce tattaunawa da ‘yan ta’adda ba tsari bane mai kyau wanda za a dogara da shi, domin a cewarshi, tattaunawa da ɗan ta’adda kamar ƙara masa ƙarfi a ke yi.

Ya ce yin hakan babu abin da zai haifar face ƙaruwar ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Ganduje ya bayyana haka ne yau Talata a wani taron manema labarai da ya gabatar. Ganduje ya ce: “An tsara hukumomin tsaro ne bisa tsari da kwarewa. Sojin sama su na da nasu tsarin aikin, haka nan Sojin ƙasa, Sojin Ruwa, yan sanda da jami’an DSS. Saboda haka, zama a ce za a yi sasanshi da ‘yan bindiga, abu ne ni da ba zan goyi bayanshi ba.

“Saboda a Najeeriya, mallakar bindiga ba tare da lasisi ba, babban laifi ne. Ta yaya a ke tsammani yan bindiga za su fito daga dajikansu su zauna da shuwagabanninsu na gargajiya, shuwagabannin kananun hukumoninsu ko ma da yan sanda a ce za a fara zaman sulhu? Ina ganin wannan tsarin da ma a ke yi, ba ya haifar da ɗa mai ido, kuma tsari zai cigaba da ƙin yin tasiri.

“Irin wannan damar ma da a ke basu, tana ƙara musu ƙarfi ne domin su na nema ne a ƙyalesu su yi wasu abubuwan, su na nema a basu kuɗi, babura da wasu abubuwan da su ke taimakawa ta’addancin nasu. Yin hakan yana ƙara basu ƙaimi wajen ayyukan ta’addanci. Ni ba na goyon bayan haka.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00