An kama wata mata da zargi sace jariri, ta kai wa danginta a matsayin ita ce ta haihu a jihar Kebbi

by Dabo Online
0 comments

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta kama wata matashiya mai shekaru 19 a ƙaramar hukumar Zuru, bisa zargin satar jariri da kuma kai shi wajen mijinta tana gabatar da shi a matsayin ita ce ta haifeshi.

Lamarin ya faru ne a ranar 23 ga Yulin 2025, inda ake zargin wadda ake zargin ta ziyarci Fatima Muhammad jim kaɗan bayan ta haihu, inda ta ce za ta taimaka mata wajen ɗebo ruwan zafi.

A cewar ‘yan sanda, wadda ake zargin ta yi amfani da wannan dama wajen guduwa da jaririn maimakon ta dawo da ruwan.

Binciken farko ya nuna cewa wacce ake zargin ta na fama da matsin lamba da tashin hankali sakamakon rashin samun haihuwa, musamman ganin yadda sauran ƙawayenta su ke da ƴa’ƴa.

‘Yan sanda sun ce ana zargin ta yaudari mijinta tsawon kimanin watanni tara, inda ta sa shi ya yarda cewa tana da ciki. Bayan haihuwar jaririn da ake zargin ta sace, sai ta kai shi wajen mijinta tana gabatar da shi a matsayin ɗansu.

An kama wadda ake zargin ne a ranar 14 ga Agustan 2026, bayan da ’yan sanda su ka gudanar da bincike na tsawon lokaci.

Daga bisani, an gano jaririn da aka sace, inda aka mayar da shi ga mahaifiyarsa ta haihuwa.

’Yan sanda sun ce wadda ake zargin tana hannunsu, kuma za a gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala bincike, kamar yadda doka ta tanada.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, CP Umar Hadejia, ya yaba wa jami’an rundunar bisa ƙwazo da ƙwarewar da su ka nuna wajen ganin an kubutar da jaririn cikin aminci tare da kama wadda ake zargin.

Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar za ta ci gaba da kare yara tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi ya fuskanci hukuncin da ya dace.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Bashir Usman, ne ya fitar da sanarwar a ranar 16 ga Agustan 2026.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00