Takaddama ta barke tsakanin Sheikh Asadussunah da Dr. Ayuba a kan abinicn masu ciwon Siga

TaƘaddama ta ɓarke tsakanin fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Asadussunah, da ƙwararren likitan sinadaren jiki na Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Ɓalewa, Dr. Ayuba Mugana, kan wani bidiyo da malamin ya fitar a shafukansa na sada zumunta.

by Dabo Online
0 comments

Takaddama ta ɓarke tsakanin fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Asadussunah, da ƙwararren likitan sinadaren jiki na Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Ɓalewa, Dr. Ayuba Mugana, kan wani bidiyo da malamin ya fitar a shafukansa na sada zumunta.

DABO FM ta tattara cewa Sheikh Musa Asadussunah ya fitar da wani bidiyo a shafukansa na sada zumunta, inda ya yi sharhi kan wasu bidiyoyin masu magana kan harkokin lafiya, ciki har da Dr. Ayuba.

A cikin bidiyon, malamin ya ce: “Tsakani da Allah, gaskiya mutanen sun raba mana hankali, masana lafiya su ƙara bincike a kai, duk da har yanzu ba mu kai abin ga ministan lafiya ba.”

Ya ci gaba da cewa; “Akwai wani mutum da ya ga ya lissafo kusan abinci 50 da ake ci a ƙasar Hausa, inda ya ce duk wanda ya ci “musiba ya ci”.

Malamin ya ƙara da cewa an kuma ce idan aka yi aure, amarya da ake kaiwa a siya mata nama kamar kaza ko balangu a tafi da shi, idan ta ci, to ta ci masifa. Ya ce abin da ya kamata idan an zo aure shi ne a siya mata kabeji a tafi da shi.

A lokacin da malamin ke bayanin wannan batu, an nuna hoton Dr. Ayuba a gefe. Hakan ne ya sa Dr. Ayuba ya mayar da martani, inda ya ce an yi masa ƙazafi saboda bai faɗi abin da aka ce ya faɗa ba.

Dr. Ayuba ya ce: “Ni ban taɓa faɗar haka ba. Duk waɗanda su ke bibiyata su na ganin bidiyoyi na, za su shaida cewa wannan maganar ba gaskiya ba ce. Ya kamata a duba wanda ya faɗi haka kafin a saka hotonsa.”

Ya kuma ba da wa’adin awa 24 da a cire hotonsa daga bidiyon, yana mai cewa rashin yin hakan zai sa ya kai ƙara zuwa wajen hukumar da ke magance irin waɗannan matsalolin ɓata suna a kafafen sada zumunta.

Sai dai bayan kallon bidiyon Sheikh Asadussunah, DABO FM ta fahimci cewa hoton da ya fito a bidiyon malamin hoton Dr. Ayuba ne daga wani bidiyo da yake magana kan amfanin ƙwai ga mai ciwon siga.

Da bidiyon da Dr. Ayuba yake magana a kan ƙwai ya ƙare, malamin bai cire hoton ba, yayin da yake ci gaba da bayaninsa kan batun abincin da ya ce wani likita (ba Dr. Ayuba ba) ya ambata.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00