Hukumar da ke hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya reshen jihar Ogun, ta kama wata tsohuwa yar shekara 101 da ake zargi da siyar da tabar wiwi.
An kama matar mai suna Esther Ogunmabo a unguwar Ilisan da ke jihar Ogun, da ɗaurin tabar wiwi kala-kala mai nauyin giram 30. Daga cikin nau’in tabar wiwin akwai mai ƙarfi da kuma wacce aka yi wa surki.
Matar ta ce ta na siyar da tabar wiwin ne ga mazauna unguwar.
Cikin wata sanarwa da hukumar NDLEA ta hannun mai magana da yawunta, Femi Babafemi, ta ce Esther Ogunmabo ta sanar da hukumar cewa ta tsunduma sana’ar siyar da miyagun ƙwayoyine bayan shagon da na siyar da kayyakin yau da kullum ya ƙone.
Jaridar Punch ta rawaito cewar; Shugaban hukumar, Birgediya Buba Marwa mai ritaya, ya bayar da umarnin a bayar da belin matar. Ya ce a kai ta wajen da za a yi mata nasiha kuma a samar mata da hanyoyin da zai sa ta nutsu don kar ta sake komawa siyar da miyagun kwayoyin.
