Gobara ta tashi a wani gini mai ɗauke da ofisoshi a Kasuwar ’Yan Canji da aka fi sani da WAPA, da ke ƙaramar hukumar Fagge a birnin Kano.
Wutar ta tashi ne a gidan Alhaji Audun Aja da ke kusa da bankin GTBank, a kan titin Murtala Muhammad, da misalin ƙarfe 1 na rana ranar Juma’a, kafin sallar Juma’a.
Wani ɗan kasuwar canji da ya yi magana da wakilin DABO FM ya ce mutanen da ke ƙasan ginin ne suka fara ganin hayaƙi daga hawa na uku.
“Mu na can ƙasan bene ne muka ga hayaƙi a hawa na uku, muka yi ƙoƙarin sanar da waɗanda su ke sama abin da ke faruwa,” in ji shi.
A cewarsa, wutar ta fara ci ne tun kafin sallar Juma’a, da misalin ƙarfe 1 na rana.
Sai dai, aikin kashe wutar bai fara ba sai bayan ƙarfe 2 na rana, sakamakon ƙalubalen samun damar shigar da motar kashe gobara cikin layin da ginin yake, a cewar bayanan da DABO FM ta tattara.
Ginin gidan Alhaji Audun Aja na da mashigai guda biyu, ɗaya daga Duni Street, ɗayan kuma yana kallon titin Murtala Muhammad, kuma manyan motocin kashe gobara ba za su iya shiga ta fuskar da ke kan Duni Street ba, hakan ya tilastawa motocin kashe gobara yin zagaye mai tsayi kafin su samu shiga Kangon da gidan ya ke.
Wakilin DABO FM da ya isa wurin ya tabbatar da cewa wutar ta ƙona wasu manyan ofisoshi da ke hawa na uku na ginin, yayin da kuma ta fara kama wasu ofisoshin da ke hawa na biyu.
A halin yanzu, ba a bayyana musabbabin tashin gobarar ko adadin asarar dukiyoyin da gobarar ta haddasa ba. Sai dai an tabbatar babu asarar rai ko rauni guda ɗaya da aka samu.
