Home LabaraiZamfara: Masu Garkuwa Sun Yi Garkuwa Da Sabbin Sojoji Uku

Zamfara: Masu Garkuwa Sun Yi Garkuwa Da Sabbin Sojoji Uku

by Dabo Online
0 comments

……, Su na Neman Kudin Fansa Nira Miliyan 50

Wasu mutane da ake zargin ’yan fashin daji ne sun yi garkuwa da sabbin sojojin kasar nan guda uku wadanda suka kammala horonsu kwanan nan. Lamarin ya faru ne a jihar Zamfara bayan da aka bayyana cewa hukumomin soji sun bar sojojin su ci gaba da tafiya da kansu zuwa jihar Kebbi, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta bayyana.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne a ranar 2 ga watan Yulin shekarar 2026, jim kadan bayan da sojojin suka kammala taron yaye dalibai na rukunin kwas na 26 (26 NA) a jihar Kaduna.

A bisa tsari, ana sa ran rundunar soji za ta kwashe sojojin daga Kaduna zuwa garin Zuru da ke jihar Kebbi bayan kammala horon na su. Sai dai maimakon a kaisu inda ya dace, an ajiye su ne a Gusau, babban birnin jihar Zamfara da yamma, sannan aka umurce su da su nemi ababen hawa da kansu domin karasa sauran tafiyar washegari.

Da safiyar ranar ce sojojin tare da sauran fasinjoji suka shiga motar haya daga tashar mota ta Gusau domin nufar jihar Kebbi. Wasu majiyoyi masu masaniya kan lamarin sun bayyana cewa yayin da motar ke wucewa ta yankin Anka a jihar Zamfara, ’yan fashin daji dauke da manyan makamai suka yi musu kwanton bauna, inda suka yi garkuwa da fasinjojin da ke ciki, ciki har da sojoji ukun da direban motar.

Da fari, masu garkuwar sun bukaci kudin fansa har naira miliyan 50, amma daga baya suka rage kudin zuwa naira miliyan 5 ga kowane mutum guda da ke tsare a hannunsu.

Iyalan sojojin da aka sace sun bayyana cewa duk da sanar da hukumomin soji game da faruwar lamarin tun bayan aukuwarsa, har yanzu ba a fara wani yunkuri na ceto su ba, sannan babu wata magana a hukumance da aka yi musu bayan kwanaki 13 da faruwar lamarin.

Wani masani kan harkokin tsaro ya tabbatar da faruwar lamarin a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, inda ya bayyana cewa ya tattauna kai-tsaye da iyalan sojojin. Ya kara da cewa sojoji shida ne ke tafiya tare bayan bikin yaye su, inda uku daga cikinsu suka tsere lokacin da aka kai musu harin. Sai dai guda daya ne kacal aka samu labarinsa cikin wadanda suka tsere, yayin da har yanzu ba a san inda sauran guda biyu suke ba.

Masanin tsaron ya bayyana cewa iyalan sojojin suna cikin matsananciyar damuwa saboda ba su da kudin da za su iya biyan kudin fansar da masu garkuwar ke nema domin ba su da komai.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00