Home LabaraiKudaden kadarorin Malami da a ka kwace za isa a gina ajujuwa 50,172 a Najeriya

Kudaden kadarorin Malami da a ka kwace za isa a gina ajujuwa 50,172 a Najeriya

by Dabo Online
0 comments

A ranar Laraba ne dai wata babbar kotun a Najeriya da ke da zama a Abuja ta bayar da umarnin kwace wasu kadarori guda 48 mallakin Abubakar Malami, tsohon Ministan shari’ar Najeriya daga 2015 zuwa 2023.

Kotun ta ce EFCC ta gabatar da ƙwararan hujjojin da su ka tabbatar da cewar Abubakar Malami bai mallaki kadarorin ta hanyoyin da su ka dace ba.

Hukumar EFCC ta ce darajar jumillar kadarorin sun kai kimanin Naira biliyan ₦213,234,120,000.

DABO FM ta lissafa cewar adadin kuɗin ya isa a gina ajujuwa masu kyau da inganci har guda 50,172 duk kuwa da tsadar kayyakin gini a Najeriya.

Mun yi lissafi ne bisa cewa ana bukatar ₦17,000,000 domin gina rukuni guda mai dauke da ajujuwa 4. Wannan yana nufin kudin gina aji guda ya kai:

₦17,000,000 a rabata gida 4 = ₦4,250,000

Saboda haka:

  • Aji 1 = ₦4,250,000
  • Ajujuwa 4 = ₦17,000,000

Idan a ka dauki jimillar ₦213,234,120,000, aka raba ta da ₦17,000,000 (kudin gina rukuni guda), za a samu:

₦213,234,120,000 ÷ ₦17,000,000 = rukuni 12,543, tare da saura ₦3,120,000.

Tun da kowanne rukuni yana dauke da ajujuwa 4, adadin ajujuwan da za a iya ginawa shi ne:

12,543 × 4 = ajujuwa 50,172.

A takaice, idan aka yi amfani da wannan lissafin, ₦213,234,120,000 za su iya gina rukuni 12,543 masu dauke da ajujuwa 4 kowannensu, wato jimillar ajujuwa 50,172, sannan kuma za a rage ₦3,120,000 da ba zai isa a gina cikakken aji ba.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00